By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce rasuwar Sarkin Jama’are, Ahmad Wabi III, daya daga cikin sarakunan gargajiya da suka fi dadewa kan karagar mulki a Afirka, “karshen zamani ne.”
Yayin da yake mayar da martani game da rasuwar Sarkin, wanda aka yi jana’izar a ranar Lahadi, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar a Abuja, Buhari ya ce, “Rasuwar sarki Ahmad Muhammadu Wabi da ya yi mulki na tsawon shekaru 50. babban rashi ne, ba ga jihar Bauchi kadai ba, har ma da kasa baki daya saboda dimbin gudunmawar da ya bayar wajen zaman lafiya ba za a iya misalta shi ba.”
“Marigayin sarkin mutum ne nagari wanda ya kwashe shekaru 50 yana yiwa al’ummarsa hidima ba tare da wani cece-kuce da ya biyo bayan gagarumin mulkinsa ba.
“Ina fatan in mika sakon ta’aziyyata ga iyalai, Majalisar Masarautar Jama’are, gwamnati da daukacin al’ummar Jihar Bauchi bisa rasuwar wannan babban basaraken gargajiya.
“Allah ya jikansa da rahama. Allah ya saka masa da Aljannah,” inji Buhari.
RIP baba sarkin jama’arre