Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Iweze dake karamar hukumar Aniocha South a jihar Delta da kuma rundunar sojin Nijeriya, ‘yan’uwa da abokan arziki bisa rasuwar Manjo Janar Cyril Iweze.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta hannun Kakakinsa, Femi Adesina a Abuja a ranar Alhamis. Inda ya bayyana Janar din sojan a matsayin mutumin kirki wanda ya zama na daban a cikin sojoji.
Buhari ya ce Marigayi Iweze ya rike mukamai daban-daban a aikinsa na soja tun daga matakin Kwamandan kamfaninsa har zuwa shugaban sashen samame a Hedikwatar sojin kasa.
Har wala yau ya taba rike mukamin shugaban ma’aikata ta ECOMOG a tsakanin 1990 da 1991.