Shugaban Kasa Buhari ya girgiza da mutuwar Ibidun Ighodalo, wata mata ‘yar yankin Kudancin Nijeriya.
Shugaba Buhari ya bayyana kaduwarsa akan mutuwar Ibidun Ighodalo wacce take mata ce ga Babban Fasto din nan Itua Ighodalo wacce ta mutu tana da shekara 40 a duniya.
Hakan na dauke ne a sanarwar da Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar. Inda ya ce shugaba Buhari ya bayyana cewa a tare za su yi jimamin wannan babban rashi da aka yi a Nijeriya.
“Mijinki Fasto Itua Ighodalo mutumin kirki ne da ya dage wajen yiwa Nijeriya addu’o’in samun zaman lafiya da karuwar arziki, kuma mutum ne da ya tura da takardar ta’aziyya kai tsaye ga fadar Gwamnatin tarayya lokacin da Abba Kyari ya rasu.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa; “Fasto ka yi hakuri da wannan babban rashin da aka yi maka, mu ma muna jin radadi a zukatanmu. Da fatan za ka daure sosai a wannan lokaci mai wahala da kake ciki na mutuwar matarka.” Ya shawarce shi.