Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa da alhininsa bisa rasuwar mahaifin Sanata Binta Masi Garba na APC.
Mahaifin na ta mai suna Garba Tizhe Tumba (Kofur mai ritaya), ya taba aiki da shugaban kasa Buhari a lokacin yana soja.
Tumba, ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da shi, inda ya rasu a Bazza dake karamar hukumar Michika a jihar Adamawa.
Ya taba zama direban Buhari a gidan soja. Shugaban kasar ya mika ta’aziyyar ne a sanarwar da Kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar a Abuja.