Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin yi wa hukumar ‘yan Sandan Najeriya gyara tare da kawo sabbin jami’an sirrin na cikin rundunar.
Daga cikin gyara da Shugaba Buhari ya amince a hukumar ya aminta da samar sa ‘yan sanda na musamman a shiyoyi biyar a fadin kasar nan.
Wannan yana fitowa ne daga wani jawabi da Sufeto Janar na kasa Muhammad Adamu ya sanyawa hannu.
https://dimokuradiyya.com.ng/kotu-ta-yankewa-wani-malamin-addinin-kirista-hukuncin-kisa/
Buhari ya aminta da wannan gyara da za a yi hukumar, kuma zai kasance shi ne jagora na jami’an na musamman, sannan gwamnonin kowace jiha zasu zama shina daga cikin kwamitin zartasawa na hukumar, sai dai Shubaga Buhari zai nemi zama da wakilan hukumar’yan sanda domin samun matsaya guda.
Wannan gyara da yayi zai kawo adadin shiyyoyin ‘yan sanda takwas kenan a kasar nan baki daya, wanda kafin nan ana guda shida ne.
Har wa yau, Buhari ya raba hukumar jami’an farin kaya ta CID zuwa shiyya biyu, wato Enugu da Gombe.