Shugaba Buhari yace Bazai bar wata Dukiya domin Ɗiyansa su Gada
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi kira ga Iyaye dasu koyawa yaran su ɗabi’a mai kyau, har da tsoron Allah, mutunta Shuwagabanni, da kuma Kyakkyawar rayuwa ta hanyar cigaba da ilmantar dasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗuminsa: Najeriya ta sanya ranar fara Jigilar Maido da Alhazan ta
Shugaba Buhari yayi wannan kiran a ranar Laraba a lokacin da ya ziyarci Fadar mai martaba sarkin Daura, Jahar Katsina domin kai mashi ziyarar Sallah.
Buhari ya yi kira ga Matasa dasu nemi ilmi, badan su samu aikin Gwamnati ba wanda babu shi, sai don su samu dabaru da yanda zasu yaƙi Talauci domin rayuwar su a ƙarni na 21.
Yace dole a samu lokaci mai yawa domin tunatar da Shuwagabannin gobe, da ilmi, da yanda Duniya ke canjawa, ta hanyar sabbin Fasahohi na zamani.
Yace Yanzu dole a baiwa koyon sana’o’i fifiko da kuma yadda za’a yi amfani da Fasahohin Zamani yana mai cewa “a lokacin cutar Covid-19 dukkanin Ma’aikata masu mataki 12 ance su tsaya a gida, kuma abun mamaki anyi aikin yanda ya kamata.
“Abinda na baiwa fifiko shine horas da yarana su zamo masu amfani. Na gayawa yarana, musamman mata, cewa zasu yi Aure bayan sun yi Digiri na farko.
“Tuni sun san bazan bar komai domin su Gada ba. Abinda na damu shine inga yarana sun samu ilmi mai kyau,” Inji shi.