By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu yana jagorantar majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya, FEC, a dakin taro na ofishin uwargidan shugaban kasa, dake fadar shugaban kasa, Villa a Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shima ya samu halattar mitin din.
Sakataren gwamnatin tarayya SGF Boss Mustapha da shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa farfesa Ibrahim Gambari dukkanin su suna daga cikin wadanda suka halaccin zaman tattaunawar.
Kazalika ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Dakta Isa Pantami da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, da Alkalin alkalai na gwamnatin tarayya da ministan shari’a Abubakar Malami da ministan Kwadago Dakta Chris Ngige.
Sauran sun hadar da ministan wutar lantarki Abubakar Aliyu da na samar da ruwan sha Suleiman Adamu da kuma ministan kasafin kudi da tsare tsare Clement Agba.
Da shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya Folashade Yemi-Esan da sauran ministocin daga bangarori da dama duk sun halacci zaman tattaunawar a Abuja.
Comments 1