By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC guda biyu, Rotimi Amaechi, ministan sufuri kuma wanda ya taba zama darakta janar na yakin neman zaben sa karo na biyu, da Nasiru Haladu Danu, fitaccen dan kasuwa, bisa kyautar da za’a yi masu ta nadin sarauta a gobe Asabar a Masarautar Daura.
Shugaba Buhari ya bayyana nadin Amaechi da lakabin “Dan Amana,” (wanda aka aminta da shi) a matsayin sadaukar da kai ga dangantakar da ke tsakanin al’adu daban-daban na kasar.
Sannan za’a nadawa Alhaji Danu rawani a matsayin Tafida Babba na Daura.
Kazalika ya yabawa Ministan “saboda yin aiki da makamashi mai yawa don ganin CANJIN da muka yiwa ‘yan Najeriya alkawari ya tabbata,” yana mai bayanin cewa “canjin da muke gani a fannin sufuri wani abu ne na ban mamaki.”
Shugaban kasar ba zai halarci taron ba, amma ya nada tawaga mai wakilai uku, wadanda suka hada da ministocin albarkatun ruwa Injiniya Sulaiman Adamu, da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika da kuma babban mataimaki na musamman kan (kafofin yada labarai) Garba Shehu amatsayin wadanda za su wakilce shi.