Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis zai fara wata ziyarar aiki zuwa birnin Yamai fadar mulkin Jamhuriyar Nijar domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki, da kuma wani zama na musamman kan ciniki cikin ‘yanci na nahiyar yankin Afirka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai fara wata ziyarar aiki a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya bayyana a wata sanarwa a ranar Larabar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Gwamna Uzodimma Ya Kori Shugaban Jami’ar Jihar Imo
Buhari zai kuma halarci taron kaddamar da Littafin Faransanci mai suna ‘Muhammadu Buhari: Kalubalen Shugabanci a Najeriya’.Buhari Zai Halarci Taron Kaddamar Da Littattafai Na AU A Jamhuriyar Niger
Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari zai halarci taron koli na AU kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki a birnin Yamai na Nijar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabinsa na kasa a taron koli na kungiyar hadin kan Afirka kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki, taron da ke karkashin taken masana’antu na Afirka: Sabunta sadaukar da kai wajen samar da masana’antu mai cike da dorewa da bunkasar tattalin arziki.
“Babban taron koli, wanda ake kira a matsayin wani bangare na ayyukan tunawa da makon masana’antu na Afirka na shekara-shekara, ana sa ran za a yi amfani da sanarwar, wanda zai nuna muhimmancin ci gaban masana’antu da sauye-sauyen tattalin arziki a nahiyar da kuma yadda za a samu ci gaba a wannan fanni.
“Ana yin bikin aduk ranar 20 ga watan Nuwamba a kowacce shekara matsayin ranar masana’antu ta Afirka, wanda Majalisar shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar hadin kan Afirka ta amince da shi a watan Yulin shekarar 1989, a Addis Ababa na kasar Habasha.”
A halin yanzu, ana sa ran zama na musamman kan AFCFTA zai yi amfani da ka’idojin Mataki na II na yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar tare da kaddamar da wasu kayan aikin aiki.
Najeriya ta ci gaba da nuna himma sosai wajen tabbatar da cikakken aikin yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirka wanda zai samar da kasuwa guda da kayayyaki da ayyuka, da ‘yanci da saukaka zirga-zirgar zuba jari da ‘yan kasuwa a fadin nahiyar.
A ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2019, Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar AfCFTA a Yamai a yayin babban zama na 12 na Majalisar da kuma kaddamar da matakin aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci.
Kasar ta amince da zama mamban kungiyar ta AfCFTA a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar 2020.
Shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama; Ministan tsaro, Maj-Gen. Bashir Magashi (mai ritaya), Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo; ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen. Babagana Monguno (mai ritaya) da Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.
Ana sa ran Buhari zai dawo Abuja ranar Juma’a 25 ga watan Nuwamba.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Isa Jihar Ebonyi, Don Kaddar Da Wani Aiki
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya isa Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi domin gudanar da gagarumar liyafar Aiki.
Tinubu, wanda ya isa wurin a kwanakin baya ya samu tarba daga Gwamna David Umahi, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, ‘yan majalisar jiha da na kasa, sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, da dimbin mabiya jam’iyyar da magoya bayan jihar.
Nan take dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kaddamar da sabon titin ‘yan biyu na gidan gwamnati da gwamnatin Umahi ta gina.