Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya takwarar shi na Jamhuriyar Nijar Mahammadou Issoufou murna bisa kammala wa’din shi na biyu kan karagar mulki lami lafiya tare da samu kyautar gwarzo daga Gidauniyar Mo Ibrahim, inda ya bayyani shi a matsayin gwarzon shugaba.
Shugaba Buhari wanda aka karrama shi da kyauta mafi girma ta kasar Nijar mai suna Grand Coix De Ordre National Du Niger ya jinjina wa shugaba Issoufou bisa jajircewar shi wajen tabbatar da tsayuwar Dimokuradiyya tare da yaba mishi bisa irin kyautata dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar.
“Ya Mai girma Shubana KAsa, Da farko dai ina mai taya ka murna bisa kammala wa’adin ka na biyu lami lafiya, ina kuma taya yan Nijar murnar kammala zabe lami lafioya ba tare da wata hatsaniya ba” A cewaqar Shugaba Buhari.
“A Zahirin Gaskiya Nasaroroi da ka cimma a yayin mulkin ka ba karamin abu ba ne, wannan ya sa daraja da kimar nka suka karade zukatan yan Nijar har ma da mu makwabta Najeriya” In ji Shugaba Buhari.
Cikin Wata sanarwa daga mai tallafa wa Shugaba Buhari kan yada labarai Mr. Femi Adesina ya fitar, ya ce ziyarar shi ta farko bayan darewar shi kan karagar mulki ita ce kasar Nijar, wanda hakan ya kuma taimaka wajen kyauata dangantakar kasashen biyu.
Daga bisani Shugaba Buhari ya bukaci Zababben shugabana KAsar Nijar daq ya dora kan nasarorin da Shugaba Mai barin gado Mahammadou Issoufou ya cimma.
Da yakae maida jawabi Shugaban KAsar Nijar Mai barin Gado Mahammadou Issou ya gode wa shugaba Buhari da ma kafatanin yan Najeriya bisa bashi goyon baya a shekaru goma da shafe yana mulki, musamman kasancewar shi a matsayin shugaban ECOWAS inda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta biyu a gurin shi bayan Nijar.