- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Indiya bisa wani mummunan hatsarin jirgin kasa.
- Tinubu yace zuciyata na mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa a hatsarin jirgin kasa mai ban tausayi.
- Hatsarin dai ya afku a ranar Juma’a baya ga wadanda suka mutu, wasu sama da 900 sun jikkata.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Indiya bisa wani mummunan hatsarin jirgin kasa da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji sama da 280 a kasar.,Daily Trust ta rawaito
Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ta hannun ‘yan jarida, ya bayyana hatsarin jirgin a matsayin mai tayar da hankali, tare da jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.
KARANTA WANNAN: Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya
“Zuciyata na mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa a hatsarin jirgin kasa mai ban tausayi a jihar Odisha ta Indiya.
“Mun tsaya tare da Indiya cikin ‘yan uwantaka a wannan mawuyacin lokaci. Girman hadarin da alkaluman wadanda suka mutu ya yi kira ga kasashen duniya su tallafa wa Indiya don daukar matakin da ya dace kan wannan mummunan hatsarin.
“Ina mika sakon ta’aziyyata ga Firaminista Narendra Modi, da mutanen Indiya da kuma iyalan wadanda suka makale a hadarin,” in ji shugaban.
Mummunan hatsarin da ya rutsa da jiragen kasan fasinja guda biyu da wani jirgin kaya a birnin Balasore na kasar Indiya, a jihar Odisha da ke gabashin kasar, ya afku ne a ranar Juma’a.
Baya ga wadanda suka mutu, wasu sama da 900 sun jikkata a wani hatsarin jirgin kasa mafi muni a tarihi.
A wani labarin kuma, Dan Wasan Gaba Na Real Madrid Ya Daura Damarar Barin Kungiyar
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Marco Asensio zai bar kungiyar.
Asenson yace dole ne ya dauki matsaya mai wahala – Na yanke shawarar shiga sabuwar hanya don neman sabon aiki
Dan wasan na Sipaniya bai tabbatar da inda zai je ba kawo yanzu.