Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja, a Laraba, zuwa Banjul, da ke Jamhuriyar Gambia, domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, bayan sake zabensa a karo na biyu.
A bisa gayyatar mai masaukin baki, shugaba Buhari zai kasance babban bako na musamman a wajen bukukuwan da wasu shugabannin kasashen Afrika za su halarta a filin wasa na ‘yancin kai na Bakau.
Shugaba Buhari tare da wasu shugabannin kungiyar ECOWAS sun taka rawa wajen maido da mulkin dimokuradiyya a Gambia a shekarar 2017 bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan ya sha kaye a zabe.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministan harkokin wajen kasar Mista Geoffrey Onyeama; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, majo janar Babagana Monguno (mai ritaya); Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa Ambasada Ahmed Rufa’i da sauran manyan jami’an gwamnati.
Ana sa ran shugaban zai dawo kasar a karshen bikin rantsarwar.