Mataimakin shugaban ƙasa farfesa Femi Yemi Osinbajo ya ƙara jaddada matsayar gwamnatin tarayya na ƙirƙiro da guraben ayyuka aƙalla miliyan biyar ga al’ummar ƙasar nan.
Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin wani taro da cibiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta jihar Lagos ta shirya wanda aka gudanar ta kafar yanar-gizo.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-tarayya-za-ta-samar-wa-da-matasa-dubu-200-aikin-yi/
Ya ce, gwamnati tana ƙoƙarin bunƙasa ɓangaren aikin noma da samar da gidaje masu rahusa da bunƙasa masana’antu wanda hakan za su taimaka wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu sha’awar zuba jari daga ƙetare dana cikin gida don rage rashin ayyuka tsakanin matasa.
Kuma yace gwamnatin tasu zata tabbatar wa da ‘yan Najeriya wannan al’amari nan ba da jimawa ba.