Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce zanga-zangar da ta barke a kasar a kwanakin nan wata makarkashiya ce, kuma hakan mugun nufi ne ga dimokuraɗiyyar kasar.
Zanga-zangar ta biyo bayan tasa keyar tsohon shugaban kasar ne Jacob Zuma izuwa gidan yari.
Kawo yanzu mutane sama da dari biyu ne suka kwanta dama, yayin da aka fara da tun farko da ɗari.
Wannan zanga-zanga dai ta yi sanadin kwasar ganima a shaguna da dama na kasar, ko da yake daga bisani yan sanda sun sanya sulke don kare masu kai abinci daban daban a fadin Afirka ta Kudun.
Hukumomi a birnin Kwazulu-Natal sun ce kwasar ganimar ta yi sanadiyyar salwantar kudi da ya kai sama da dala biliyan daya yayin da aka farfasa shaguna sama da 800.
Sai dai shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya ce da ma wannan zanga-zanga shiryayya ce kawai don nakasa dimokuradiyar kasar, kuma ya ce an gano masu hannu cikin kitsa ta.