Kungiyar Hadin Kan Matasa a Siyasa (YIP) a ranar Asabar ta nuna goyon bayanta ga Sanata Sani Musa, a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.
A cikin wata sanarwa da Olusegun Oshaji, Darakta Janar na YIP ya fitar a Abuja, ya ce zabin kungiyar na Sani amincewar hadin gwiwa ne domin taimakawa ci gaban kyawawan ayyukan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a karkashin jagorancin APC.
“Mun yi imanin cewa Sanata Musa shi ne mutumin da zai ci gaba da kyawawan manufofin gwamnatin Shugaba Buhari tare da bude sabon shafin zaɓen shugabanni wadanda za su hada kan nasarorin da jam’iyyar ta samu.
“za a dawo da layin dogo da aka yi watsi da shi, gina hanyoyi da gadoji da shirye -shiryen saka hannun jari na domin bunkasa walwalar al’umma da Shugaban kasa ke aiwatar wanda zai dorar da shi.
“Shugaba Buhari ya samu nasarori da yawa ta hanyar hadin gwiwa da bangaren shari’a da majalisar dokoki; kawai ya dace a zabi shugaba na gari mai amana don ci gaba da irin wannan lokacin, a karkashin inuwar jam’iyyar.
Ya bayyana Musa a matsayin mai gina al’umma kuma mai hankali wanda zai iya haɗa ƙoƙarin da kwamitin riƙo na jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya yi.