Wannan na zuwa ne yayin da fitaccen ɗan wasan na Argentina mai shekara 34, wanda ba shi da yarjejeniya tun 1 ga watan Yuli, ke fatan sabunta yarjejeniya domin tsawaita zamansa na shekara 21 a Barcelona.
Barcelona ta ce a ranar Alhamis ya kamata Messi ya sa hannu kan yarjejeniyar, amma aka samu cikas ga dokoki da sharuɗan kuɗi na hukumomin La Liga.
Yanzu haka dai masu sha’awar kwallon kafa a duniya sun zura idanu ne kan ganin makomar Messi a nan gaba, musamman yadda a yanzu ya kasance ba shi da kungiya.
Ko da yake har yanzu babu wata kungiya da ta yi tayi wa ɗan wasan ƙwallon ƙafar, to amma an ce mai kyau ba ya talla, la’akari da irin yanayin dan wasan.
Messi dai ya share shekara 18 yana murza leda a Barcelona, zaman da ya sa ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau bakwai a Ƙungiyar.