Rabaran Supo Ayokunle, shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa wato CAN, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rika nuna soyayya da hadin kai ga juna domin ci gabantar da Nijeriya.
Rabaran Ayokunle ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kawo wa mai Martaba Sarkin Zazzau, Dr Shehu Idris a ranar Talata a garin Zariya dake jihar Kaduna.
Ziyarar da shugaban CAN din ya kawo, na daya daga cikin ziyarorin da ya shirya yi a fadin jihohin kasarnan.
Ayokunle ya ce kiran ya zama wajibi domin da yadda idan aka yi amfani da dabi’un mutunta juna, tare da mutunta addinan juna, hakan zai taimakawa ci gaban kasa.
Ya bayyana cewa ya yi imanin cewa duk da matsalolin da Nijeriya ke fuskanta ta fuskancin tsaro da sauran matsaloli, amma a cewarsa Nijeriya ba za ta tarwatse ba, a maimaikon tarwatsewa, za ta samu ci gaba ne.
Ya jinjinawa Sarkin Zazzau, bisa kyakkyawan shugabanci da yake nunawa al’ummar Zazzau. Inda ya bayyana kasar Zazzau a matsayin muhalli da ke samun ci gaba duk da irin dimbin al’umma masu fahimta da kabila daban-daban da ta hada.
Da yake maida jawabi, Sarkin Zazzau din, ya bayyana jindadin bisa ziyarar shugaban CAN din, inda ya shawarce shi da ya ci gaba da bunkasa zaman lafiya, kuma ya tabbatar masa da cewa kofarsa a bude take koyaushe domin bayar da shawarwari.