Shugaban Faransa Emanual Macron ya isa Kasar Aljeriya a yau Alhamis inda yake fatan gyara alaƙar da ke tsakanin kasashen biyu, kasencewar man fetur da gas din da kasar ke fitarwa yana tasiri sosai ga yankin Nahiyar Turai, sakamakon fuskantar kalubale da yankin ke yi a bangaren makamashi.
BBC ta ruwaito cewa, Ziyar ta Shugaban kasar ta Faransa na zuwane bayan an dauki lokacin mai tsawo ana zaman dar dar saboda tunawa da fafutikar da kasar tayi wurin neman yanci kai wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama.
Idan dai ba a manta ba, tun a farkon wannan shekarar kasar Algeriya ta mayar da Jakadan Faransa gida.
Amma sai dai daga baya kasashen biyu sun nuna bukatar su ta neman an sake jaddada alaƙar dake tsakanin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: ‘Yan sanda Sun Rufe Hedikwatar NNPP, Sun Kama Dan Takarar Sanata
Kamar yadda fadar gwamnati Algeriya ta Elyesse ta bayyana shugaba Macron na ziyarar ne domin sake dawowa da tare da karfafa a laƙar da ke tsakanin kasashen biyu.
Fadar ta kara da cewa yana tare da rakiyar mutum 90, waɗanda suka haɗa da ministoci , shugabanin yan kasuwa, da fitattun a bangaren wasanni.
A watan jiya ne Faransa ta fusata Algeriya da makwabciyar ta Morocco, bayan da ta rage yawan bizar da take bayarwa ga matafiyan da suka fito daga ƙasashen.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani bayan da kasar tayi ikirarin cewa duka kasashen arewacin Afirka na kawo cikas wajen dawo da ‘bakin haure, da aka samu sunje Faransa ba bisa ka’ida ba.
Rikicin diflomasiyya ya fara tabarbare ne tun a watan Oktoban da ya gabata.
Sai dai masu sharhi sun ce shugaban na Faransa zai fuskanci matsin lamba kan ya yi wa al’umma wani jawabi wanda zai nuna amincewa da nuna damuwa game da yadda ake tunawa da yakin ‘yancin kailn ƙasar ta Algeriya.
Haka kuma sun ce babban makasudin wannan ziyarar shi ne samar da yanayin da za a kara yin hadin gwiwa a kan lamarurranda da suka shafi tattalin arziki da kuma tsaro.