Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce dakarun kasar sun yi nasarar kashe wani shugaban kungiyar IS a Yankin Sahara Adnan Abu Walid al-Sahrawi da Amurka ke nema ruwa ajallo saboda kazamin harin da ya kai wa sojojin ta da kuma jami’an agaji.
Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana kashe Adnan Abu Walid al-Saharawi da sojojin Faransa suka yi a matsayin wata gagarumar nasarar da suke samu akan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Al-Saharawi na da hannu wajen kashe ma’aikatan agajin Faransa a shekara ta 2000, yayin da Amurka ta bayyana neman sa sakamakon kazamin harin da aka kaiwa sojojin ta a Jamhuriyar Nijar a shekarar 2017 inda aka kashe wasu daga cikin su.
Ana zargin kungiyar IS a Yankin sahara da kai akasarin hare haren ta’addancin da ake samu a kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, wadanda ake yawan kashe fararen hula da sojoji.
Kasar Amurka ta sanya ladar Dala miliyan 5 akan duk wanda ya bada bayanan inda za’a same Sahrawi saboda hannun da yake da shi wajen kai harin ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2017 wanda ya kashe sojojin Amurka 4 da na Jamhuriyar Nijar guda 6, bayan kashe ma’aikatan agajin Faransa guda 6 tare da yan Nijar dake rakiyar su da kuma direban su ranar 9 ga watan Agustan shekara ta 2000.