Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya musanta wani rubutu da aka wallafa a Facebook, inda ya ce ya shawarci Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, da ya baiwa Peter Obi dama.
A wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Talatar nan, Akufo-Addo ya ce bayani game da Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), karya ne kuma yaudara ce.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban Ghana ya ce shi bai rubuta irin wannan batu ba kuma ba zai taba tsoma baki cikin harkokin cikin gida da siyasar Najeriya ba.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/shugaban-jamiyyar-apc-yayi-allah-wadai-da-yunkurin-wasu-yan-majalisa-kan-tsige-buhari/
“An jawo hankalina ga wani rubutu mai tayar da hankali da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda ake zargin na rubuta wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a shekarar 2023, Asiwaju Bola Tinubu, cewa ya baiwa Peter Obi dama sannan ya nemi magani ga lafiyarsa. ‘,” Akufo-Addo ya rubuta.
“Wannan gaba ɗaya karya ce kuma ɓarna ce, ba tare da sanin gaskiyar komai a ciki ba.
“Ban rubuta wa shugaban APC irin wannan wasika ba, kuma hakan ba zai same ni ba.
“Ghana da Najeriya na alfahari da shekaru masu yawa na zumunci, mai karfi da ‘yan uwantaka, kuma ni ba zan zama mai tsoma baki a harkokin cikin gida da siyasar Najeriya ba.”
An ja hankalina kan wani rubutu mai tayar da hankali da ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, inda ake zargin cewa na rubuta wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, cewa “ya baiwa Peter Obi dama sannan ya nemi lafiyarsa” 1/3 pic.twitter.com/qdDkyNNbtz
– Nana Akufo-Addo (@NAkufoAddo) Agusta 9, 2022
(SOLACEBASE)