By Ishaq Dabai
Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar, Abdulrazak Datti Salih GBi da ya bayyana a gabanta dan gane da yadda ayyukan hukumar yake tafiya.
Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma mamba mai wakiltar karamar hukumar Warawa Labaran Abdul Madari, cikin wani yanayi da ya shafi al’umma, ya gabatar da bukatar gayyatar tasa a yayin gudanar da zaman majalisar na yau Litinin.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa kudurin ya sami goyan bayan mataimakin shugaban masu rinjaye, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, mamba mai wakiltar mazabar Tudun Wada.
Majalisar ta amince da kudurin, kuma nan take Kakakin majalissar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya sanar da gayyatar Shugaban daya bayyana a gaban majalisar a gobe 14 ga watan Satumbar 2021.