Babban Daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Manjo Janar Shu’aibu Ibrahim, ya kaddamar da wani injin buga littattafai na zamani a Kaduna.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, Janar Shu’aibu ya bayyana kamfanin buga littattafai a matsayin wani muhimmin ci gaba a kokarin hukumar na sake karfafa ayyukan ta.
Ya ce, aikin, wanda aka yi shi kusan shekaru goma da suka gabata, yana daya daga cikin muhimman abubuwan da manufofin gwamnatinsa suka sa a gaba, inda ya ce, “Ma’aikatar ta buga littattafai za su kasance tabbataccen hanyar samun kudaden shiga tare da karuwar kudaden da ake turowa daga asusun gwamnatin tarayya.
“Kudaden da za a samu daga Kamfanin buga littattafai, za su magance matsalar karancin ababen more rayuwa a cikin shirin NYSC, tare da inganta horarwa da samar da jarin fara aiki ga mambobin kungiyar matasa a karkashin shirin samar da fasaha da bunkasa kasuwanci na shirin.”
Ya kara da cewa, injin buga littattafai da makamantansu da za a yi a sauran shiyyoyin kasar nan, za su kasance a bude ga jama’a domin kayo aiyukansu,
Ya kuma bukaci manajojin da su kula da wurin yadda ya kamata domin biyan bukatun hukumar ta NYSC da sauran jama’a a yankin Arewa maso Yamma.