Shugaban jam’iyar PDP reshen jihar Legas Dominic Adegbola ya rasu.
Adegbola ya rasu ne a yau Laraba kamar yadda Mai magana da yawun jam’iyar Barr. Taofik Gani ya bayyana, inda ya ce, Shugaban jam’iyar ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, da yayi jinya a babban Asibitin Gbagbada dake Legas.
Dominic Wanda ma’aikacin kiwon lafiya ne, ya fara harkan siyasa tun lokacin Jam’iyar AG ta Marigayi Chief Obafemi Awolowo da ya jagoranta.
Ya kuma rike kujerun siyasa da dama, da suka hadar da jami’in jam’iyar SDP a jihar Legas, Shugaban PAC da kuma Shugaban APN.
KARANTA WANNAN LABARIN; An Saka dokar Hana fita na away 24 a Karamar hukumar Jos ta Arewa
Kazalika ya kuma nemi takarar kujerar Gwamnan jihar Legas karkashin inuwar jam’iyar APGA, ya kuma yi takarar kujerar Sanatan Legas ta Yamma a Jam’iyar SDP, inda suka fafata da Asiwaju Bola Tnubu
Hukuncin babban Kotun jihar Legas ne ya sanya Marigayin zama Shugaban Jam’iyar PDP a jihar.
A wani labarin Kuma na daban.
Biyo bayan rikicin shugabanci da ake Samu a Jam’iyar adawa ta PDP, Gwamnonin da aka zabesu a inuwar jam’iyar, za su yi wata ganawa a gobe Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.
Taron na gaggawa zai gudana ne karkashin jagorancin Shugaban kungiyar gwaunonin jam’iyar PDP, kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. Bayan ji ta bakin takwarorin shi, a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Daraktar Janar na kungiyar Honorabul C.I.D Maduabum.
Makwanni biyu kenan bayan gwamnan ya gana da kwamitin amintattu na jam’iyar, domin magance matsalar rikice-rikicen Shugabancin jam’iyar. Bayan wani sabon rikicin da ya balle a jam’iyar sakamakon Kotu ta haramta wa Shugaban jam’iyar na kasa Prince Uche Secondus daga ai’yana kanshi amastayin Shugaban jam’iyar na kasa.
Hakan ya janyo jiga-jigan jam’iyar biyu Yemi Akinwonmi daga yankin Kudu, da Sanata Suleiman Nazif daga Arewacin Kasar nan, nuna bukatar su na neman Shugabancin jam’iyar.
Har’ilayau sanarwar ta ce, ” shugaban kungiyar Gwamnonin PDP kuma Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal CFR, tare tuntubar takwarorin shi, sun shirya wani zaman gaggawa da zai gudana a ranar Alhamis 26 ga watan Augustan shekarar 2021, da musalin karfe 5 na yammaci.”
“Taron zai tattuna sabbin batutuwan jam’iyar ta PDP” inji sanarwar.
Kazalika “kungiyar Gwamnonin na bukatar dukkannin mambobin jam’iyar, da kuma masu ruwa da tsaki da su ci gaba da hakuri, a yunkurin kungiyar na ganin ci gaban jam’iyar”