A nan gaba kadan ne cikin wannan watan ake sa ran shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier zai kai wata ziyarar aiki ga sabuwar gwamnatin haɗa ta kasar Isra’ila.
A yau Litinin ne ofishin shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa dake tabbatar da wannan labari.
Ziyarar ta wuni uku zai kaita ne daga ranar 30 ga wannan watan na Yuni zuwa ranar 2 ga watan Yulin goben.
Ana san ran Steinmeier wanda ya wa’adi biyu kan karagar mulkin Jamus karkashin Waziriya Angela Markel zai tattauna muhimman batutuwan Diplomasiya da sabon shugaban kasar ta Isra’ila.
Rabon Steinmeier da Isra’ila tun a watan Janairun 2020 bayan da ya kai ziyarar cika shekara 75 da kisan kiyashin da aka yi wa yan Nazi.
Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne majalisar dokokin Isra’ila ta jefa kuri’ar naƙi kan shugaban kasar Benjamin Netanyahu bayan shafe shekara 12 yana matsayin Firaminista.
Comments 1