Shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Jan Gotip, ya shaki iskar Yanci kwanaki kadan bayan yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred ne ya tabbatar wa manema labarai sakin wanda shugaban, ya kuma kara da cewa an sako Henry ba tare da jin rauni ba a daren jiya Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: PDP Ta Nada Wabara A Matsayin Sabon Shugaban BoT Na Jam’iyyar
Dimokuradiyya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da shugaban a ranar Laraba, a gidansa da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.
Alfred ya ce, “Shugaban karamar hukumar ya sake haduwa da iyalansa kuma nan ba da dadewa ba rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane za ta tattauna da su domin samar da bayanan sirri da za su kai ga cafke wadanda suka sace shi.
“Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Filato, CP Bartholomew N. Onyeka, ya nanata kudurin rundunar na mai da jihar ta zama wurin zama ga daukacin mazauna Filato. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da bayanan da suka dace domin su ba su damar mayar da martani cikin gaggawa kan aukuwar lamarin.”
A WANI LABARIN KUMA: Atiku Ya Gaya Mun Cewa Dole Ayu Ya Sauka Daga Mukaminsa— Nyeson Wike
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Alhamis ya dage cewa dole Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar PDP.
Wike ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shaida masa da kansa lokacin da ya lashe zaben fidda gwani a watan Mayu cewa dole Ayu ya bar mukaminsa na shugaban jam’iyyar.