Gwajin da aka yi wa Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez ya tabbatar da yana ɗauke da cutar korona duk da cewa an yi masa allurar rigakafin cutar.
Mista Fernandez, mai shekara 62, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana cikin yanayi mai kyau duk da yana ɗan jin
Amma ya ƙara da cewa gara ce ya gama bikin ranar haihuwarsa ba tare da samun irin wannan labarin ba.
A watan Janairu aka yi wa Mista Fernandez rigakafin korona ta Sputnik da Rasha ta samar, shugaba na farko daga yankin Latin Amurka da aka yi wa rigakafin.