Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo na wata ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke a Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock.
Mista Duke ya dira gidan Gwamnatin ne da misalin karfe 4:30 na yamma inda ya mike kai tsaye zuwa ofishin mataimakin Shugaban Kasar.
Ko da yake har yanzu babu takamaiman menene Dalilin ganawar tasu, amma wani Makusancin Ofishin Mataimakin Shugaban Kadar ya ce ganawa ce ta kashin kai.
Shi dai Mista Duke ya jagoranci Cross River ne daga shekarar 1999 zuwa 2007 kuma ya yi fice Gurin yawon shakatawa.
Kazalika a shekarar 2019 ya kasance dan takarar shugabancin Kasa karkashin inuwar Jam’iyyar SDP