Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a sauke tutar kasar kasa-kasa bayan rasuwar tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya, Cif Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha ya fitar a daren ranar Talata.
Sanarwar ta ce umarnin ya fara aiki ne daga ranar Laraba 12 zuwa Juma’a 14 ga watan Janairu a matsayin girmamawa ga tsohon shugaban kasar wanda ya rasu a ranar Talata 11 ga watan Janairun 2022 yana da shekaru 85 a duniya.
Solacebase ta ruwaito cewa Shonekan ya karbi mulki daga hannun Janar Ibrahim Babangida a ranar 26 ga watan Agustan 1993, amma marigayi Janar Sani Abacha ya hambarar da gwamnatinsa a ranar 17 ga Nuwamba, 1993.
Rahotanni sun bayyana cewa Abacha wanda a lokacin yana Sakataren Tsaron gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Shonekan, ya yi wa shugaban ING karin haske game da rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan dangane da soke zaben 12 ga watan Yuni kafin ya karbe mulki daga hannun sa.