Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da kaddamar da sabuwar hukumar da aka kafa a kamfanin man fetur ta Kasa (NNPC).
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a ranar Talata a wata sanarwa mai taken ‘Dakatar da kaddamar da sabuwar hukumar NNPC LTD’.
Ya bayyana cewa an dakatar da kaddamar da hukumar da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba har abada.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da kaddamar da sabuwar hukumar da aka kafa ta kamfanin man fetur na Kasa (NNPC) wanda aka shirya gudanarwa ranar Laraba 24 ga watan Nuwamba, 2021 har sai wani lokaci,” in ji Mustapha.
“Za a sanar da sabuwar ranar da za a kaddamar da hukumar nan gaba. Muna matukar nadamar rashin jin dadin da aka samu ga mambobin da wannan dakatarwar ta shafa.”
Dakatar da kaddamar da hukumar ya zo ne watanni biyu bayan kafa kamfanin mai na NNPC kamar yadda shugaban kasa ya ba da umarni.
A wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Satumba, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba ya bada umarnin a matsayin sa na ministan albarkatun man fetur.
“Wannan ya yi dai-dai da sashi na 53(1) na dokar masana’antar man fetur (PIA) na 2021, wanda ya bukaci Ministan albarkatun man fetur ya yi shigar da kamfanin NNPC cikin watanni shida da fara dokar.