A ranar Asabar din nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga taron hadin gwiwa na Turkiyya da Afirka da ya bayar da goyon baya na hakika don taimakawa wajen dakile ayyukan ta’addanci da tada kayar baya a nahiyar Afirka.
Ya sanar da taron a zama na uku na taron kolin da aka yi a Istanbul cewa, kungiyar ta’adda ta Boko Haram, duk da cewa ta wargaje da rigingimun cikin gida da kuma kasrata da sojojin Najeriya suka yi, amma ta ci gaba da kai hare-hare a wurare masu sauki.
Shugaban ya bayyana cewa taron da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira ya yi la’akari da batun ta’addanci, tare da mai da hankali kan ci gaba da samar da ababen more rayuwa a Afirka.
“Wani fanni da wannan kawancen ya kamata ya mayar da hankali a kai shi ne kalubalen da duniya ke fuskanta na sauyin yanayi wanda ke damun mu a Najeriya, Turkiyya, a fadin Afirka, da ma duniya baki daya,” kamar yadda kakakinsa, Garba Shehu ya ruwaito. “Ya zama sanadin tashin hankali ta hanyar rashin abinci, bushewar tafkuna, asarar rayuka, hijirar matasa da dai sauransu.
“Halin da ake ciki iri daya ne a duniya inda al’ummomin suke fama da gobarar dazuka, da ambaliyar teku, da ambaliya, da fari, da kwararowar hamada. Ina so in yi amfani da wannan dama don yin kira ga goyon bayan ayyuka irin su babbar ganuwa ta Afirka kan muhalli da sarrafa filaye, wanda aka tsara don yakar illolin sauyin yanayi da kwararowar hamada a Afirka.
Shirin na da nufin mayar da kadada miliyan 100 na barnatar kasa a cikin kasashe 11 na yankin Sahel-Sahara, da kama tan miliyan 250 na carbon da samar da ayyukan yi miliyan 10 na kwarai nan da shekarar 2030.”
Dangane da annobar cutar korona a duniya, shugaba Buhari ya bukaci kasashe da su yi koyi da hadin gwiwar kasashen Afirka da Turkiyya, wanda ke jaddada hadin kai da goyon baya wajen tinkarar kalubalen.
A cikin kalamansa, “Cutar annoba kalubale ce ta duniya wacce ke kira ga hadin kan duniya da mafita kuma tsarin hadin gwiwar Afirka da Turkiyya ya zama abin misali ga duniya. Ba wai kawai an sami goyon bayan juna don magance cutar ba har ma da goyon bayan juna don gina juriya da ci gaba mai dorewa a wasu sassa.
“Muna kuma yaba wa kungiyar Tarayyar Afirka bisa kyakkyawar rawar da take takawa wajen daidaita tsarin aiwatar da kawance.”
Shugaban ya yi nuni da cewa, la’akari da yanayin kalubalen da duniya ke fuskanta a wannan zamani na rashin tabbas, dole ne shugabannin kasashen duniya su ci gaba da sanya jin dadin ga bil’adama a tsakiyar ajandar samar da moriyar jama’a da wadata ga kowa da kowa.
“Saboda haka dole ne mu inganta kimiyya, fasaha, da kirkire-kirkire tare da raba ilimi daga bincike da ci gaba don samar da kayan aiki mafi kyau don magance kalubale na yanzu da na gaba ta hanyar da ta dace kuma mai dorewa.
“A game da wannan, Najeriya ta amince da sanarwar taron kolin da kuma shirin hadin gwiwa na 2022-2026,” in ji shi.
Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa kasuwancin kasa da kasa ya kasance injin ci gaba da dorewar ci gaban tattalin arziki, da kuma kawar da talauci a duniya.
Ya yaba da karuwar alkaluman ciniki tsakanin kasashen Afirka da Turkiyya, sannan ya bukaci yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta nahiyar Afirka (AFCTA) da ta taimaka wajen kara habaka shi zuwa matakin nasara ga dukkan kasashe.
“Muna da kwarin gwiwar cewa idan aka yi la’akari da matakin bude kofa ga kasashen Afirka da Turkiyya, wannan tsarin hadin gwiwa zai kawo sauyi ga kasashenmu da kuma dora mu kan turbar ci gaba mai dorewa ga al’ummominmu.” Shugaban wanda ya yaba wa Shugaba Erdogan bisa kafa kawancen Turkiyya da Afirka tun daga 2008.