A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke jagorantar taron kwamitin tsaro na kasa (NSC) a fadar shugaban kasa dake Villa a Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, sai Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da babban hafsan tsaro (CDS), Janar Lucky Irabor.
Haka kuma a wajen taron akwai shugaban hafsan soji, da hafsan hafsoshin ruwa da hafsan hafsoshin sojan sama, da kuma babban sufeto na ‘yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, da uwargidan ADC, Dr. Hindatu Bashir.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kafin a fara taron, shugaba Buhari ya yi wa maitaimaka masa Laftanar Kanar Yusuf Mukhtar Dodo ado da sabon mukaminsa na Kanal.