Shugaban kungiyar al’adun Yarabawa, Afenifere, Ayo Adebanjo ya ce dan takarar shugaban kasa, a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya fi Bola Tinubu na jam’iyyar APC, da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Adebanjo ya ce Obi ya fi Tinubu da Atiku a fannin “siyasa a ka’ida.”
Ya bayyana cewa gaskiya da adalci, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya fi Tinubu da Atiku.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban na Afenifere ya lura cewa ’yan siyasa ba za su je ko’ina ba idan suka kauce wa irin wannan ka’ida.
Karanta kuma: Abin Da Bisi Akande Ya Rubuta Game Da Atiku, Tinubu, Kan Takarar Musulunci da Musulmi A 2007
Ya jaddada cewa watakila Obi ba shi da karfin kudi na Atiku da Tinubu, amma ya fi su.
Adebanjo ya ce, “Ina maganar siyasa ce ta ka’ida. Na san Peter bai samu dalar Tinubu ba ballantana dalar Atiku.
“Abin da nake cewa shi ne ya fi sauran ‘yan takarar biyu. Kuma ba ina maganar jakunkunan da Tinubu ko Atiku za su iya dauka ba a yanzu.”
“Ina magana ne kan ka’idar adalci da gaskiya. Duk lokacin da kuka kauce daga siyasar ka’ida a kasar nan, ba za ku isa ko’ina ba,” kamar yadda ya shaidawa Sun, DAILY POST ta rawaito.
A wani labarin kuma: Yanzu-Yanzu: Idan Ka Isa Kana da Lafiya kazo a tattauna na tsawon Awa guda a TV — Atiku Ya Ƙalubalanci Tinubu
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Ɗan Takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Ahmed Tinubu, daya kawo kansa suti hira ta tsawon sa’a guda a gidan Talabijin.