Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ba zai yiwu ya je ko ina ba a faɗin ƙasar nan saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga.
Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka ta cikin wata hira da BBC tayi da shi, daidai lokacin da yan ƙasar ke bayyana ra’ayoyin su kan yanda matsalar tsaro ke addabar Arewacin Nigeria.
Dimokuradiyya ta bada rahoton cewa, a makon da ya gabatar ne wasu matafiya 23 suka rasu a cewar rundunar ƴan Sanda a jihar Sokoto ta hanyar ƙonewa a cikin motar da suke tafiya da nufin yin balaguro, yayin da aka kashe Kwamishina guda a jihar Katsina.
Wasu jihohi fiye da 5 a Arewacin Najeriya suna fuskantar wannan matsala ta tsaro yayin da al’umma suka hangi shugaban ƙasar a wajen taron ƙaddamar da wani littafin tarihin mutum daya maimakon zuwa jajantawa iyalai da yan uwan wadan da aka kashe.