By Ishaq Dabai
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon darakta Janar na shugaban hukumar kula da cutuka masu ya duwa NCDC Dakta Ifedayo Morayo Adetifa.
Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau litinin, Dakta Adetifa dai ya maye gurbin Dakta Chikwe Ihekweazu wanda a yanzu shine shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO a sahen cibiyar kula da annoba da fasaha wanda take a birnin Berlin na kasar Germany.
Kamar yadda ya wallafa a shafin makarantar kiwon lafiya dake birnin London, Dakta Adetifa yace “ya karbi kwalin digirin sa farko a jami’ar Ilorin dake jihar Kwara a kan harkar likitanci, sannan ya kammala karbar horo a asibitin koyarwa na Idi-Arabi dake jihar Legas.
“Kazalika nayi karatun digri na biyu MSc a fannin ilimin cututtuka sannan natafi zuwa karatun digri na uku PhD a dai fannini ilimin cututtuka a jami’ar Amsterdam dake Netherlands.