Shugaban kasa Muhammadu buhari ya taya sabon gwamnan jihar Anambra Prof. Charles Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA murna bisa nasarar lashe zaben gwamnan jihar aka kammala gudanar dashi a makon nan.
Shugaba Buhari ya taya shi murna ne a yau, bayan da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da cewa Farfesa Charles Soludo ne yayi nasara da kuri’u sama da dubu dari.
DUBA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Ƴan Majalisar Dokokin Filato Sukai Zuciya Nesa
Kazalika shugaban kasar ya kuma mika godiya ga jami’an tsaro baki daya da suka byar da gudunmawar da ta kamata wajen tabbatar da zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, tare da jinjinawa hukumare zabe bisa gudnar da ayyukanta cikin kwarewa da kuma sauri.
A karshe ya bukaci gwamnan da sauran masu ruwa da tsaki a jihar da suyi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya, wanda wasu tsiraru ke cigaba da fafutukar ganin hakan bata tabbata ba.