Shugaban Sri Lanka ya yi murabus daga muƙaminsa bayan ya fice daga kasar zuwa Singapore, saboda yawaitar zanga-zangar masu adawa da gwamnatinsa.
An yi amanna cewa shugaban ya ƙi yin murabus tun kafin ficewarsa daga kasar, saboda fargabar cewa sabuwar gwamnatin da za a kafa za ta iya kamashi.
Tsadar Abinci da man fetur da sauran muhimman bukatu ne dai suka haddasa gararumar zanga-zanga a kasar.
Dubban masu zanga-zanga a Colombo babban birnin kasar, sun yi ta raye-raye domin nuna murna bayan samun labarin murabus din shugaban.
Da fari dai Mista Rajapaksa ya fice zuwa kasar Maldives ne kafin daga bi-sani ta wuce zuwa Singapore.
Rahotonni na cewa shugaban na tare da matarsa da masu kare lafiyarsa guda biyu.
A wani lamarin kuma
Kansilolin PDP sun koka kan yawaitar kashe-kashe a Kudancin Kaduna
Kansilolin Jam’iyyar PDP daga yankin Kudancin Kaduna sun koka kan yawaitar hare-hare akan Al’ummomin su da ƴan ta’adda suke cigaba da yi.
Wannan na zuwanm ne a yayinda Kansilolin suka yanke hukuncin cewa Ɗan Takarar Sanata a yankin na Shekarar 2023, Barister Sunday Marshall Katung yana da hadin yadda za tabbatar da samun tsaro a yankin.
Da yake jawabi a lokacin taron Manema Labaru a ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Kansilolin Hon. Obed Danjuma Gankon yace yankin Kudancin Kaduna, kamar sauran yankuna a Jahar, yana fama da matsalar ƴan Ta’adda.
“Wannan ƴan ta’addan sun tada al’ummatai, sun yiwa mata fyaɗe, sun kashe tare da sace mutane, ciki har da yara. Sun lalata Al’ummomi, sun yara ba tare da gidaje ba,” Inji shi.
Gankon wanda yana tare da dukkanin Kansilolin PDP da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin Kaduna ta Kudu, yace sun amince Katung ya wakilce su a Shiyyar.