Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce a ranar Asabar Masana kiwon lafiya sun gwada shi Kuma sun tabbatar ya dauke da cutar Covid-19 amma ba ya fuskantar wasu munanan alamu.
“Bayan mun fuskanci wasu kananun alamun cutar, ni da matata an gwadamu Kuma mun kamu da cutar Covid-19., “in ji shugaban a cikin wani sakonsa na twitter.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya ta ce akalla ‘yan Najeriya 40 ne suka mutu a watan Janairu sannan kuma ma’aikatan lafiya hudu sun kamu da cutar bayan bullar cutar zazzabin Lassa a Najeriya, kamar yadda hukumar ta rawaito.
Hakan ya faru ne yayin da hukumar yaki da cututtuka ta kara da cewa a halin yanzu tana raba kayayyakin jinya ga jihohi da cibiyoyin kula da lafiya.
Jaridar Dimokuradiyya a ranar Asabar ta ruwaito cewa cutar zazzabin Lassa, cuta ce da ke yaduwa a Najeriya a duk shekara amma ana samun karuwar kamuwa da cutar a lokacin noman rani.
Hukumar NCDC a shafinta na yanar gizo ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su “ci gaba da kasancewa da yawan zargin cutar zazzabin Lassa, su yi taka tsantsan da kuma lura da alamun zazzabin Lassa. Ba duk zazzaɓi ba ne zazzabin cizon sauro”, in ji cibiyar kula da cutar.
Tun bayan bullar cutar ta karshe a shekarar 2016, NCDC ta lura cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar.
A shekarar 2019, cibiyar ta ce an samu bullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da adadin mutane 1,165 da suka kamu da cutar a kololuwar annobar.
A baya dai jaridar PUNCH ta bayar da rahoton cewa gwamnatin tarayya ta sanar da fara daukar matakin gaggawa kan cutar.
Hukumar NCDC ta ce aikin ya zama dole ganin yadda aka samu karuwar masu dauke da cutar zazzabin Lassa a fadin kasar nan.
A watan Janairu, cibiyar ta bayyana cewa mutane 40 da suka mutu da kuma 981 da aka samu a watan Janairun 2022 sun kasance a fadin kananan hukumomi 43 a cikin jihohi 14.
Cibiyar ta lura da cewa, “A tara daga mako na 1 zuwa mako na 4, 2022, an samu rahoton mutuwar mutane 49 tare da adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 19.0 cikin dari.
“A dunkule a shekarar da muke ciki ta 2022, jihohi 14 sun sami akalla guda daya da aka tabbatar a kananan hukumomi 43. Daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 82% sun fito ne daga jihohin Ondo (30%), Edo (27%) da kuma Bauchi (25%).
“Rukunin mafi rinjayen na masu shekarun da abin ya shafa sune daga 21 zuwa shekara 30 sannan kuma (iyaka daga shekara 1 zuwa 80 sai matsakaitan shekaru Tsakanin 30).
“Yawancin wadanda ake zargi sun karu idan aka kwatanta da wanda aka rawaito a lokaci guda a cikin shekarar 2021”
Cibiyar ta kuma lura da cewa, “ma’aikatan kiwon lafiya hudu sun kamu da cutar ya zuwa yanzu, 233 sun kamu da cutar, 617 kuma an jera sunayen 968 suna daga cikin wadanda ake bin diddigin su”.
NCDC ta bayyana jihohin da ake zargin sun kamu da cutar kamar haka Edo, Ondo, Bauchi, Benue, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Ebonyi, Plateau, Cross River, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun. Kwara, Legas, Delta, Gombe, FCT, Nasarawa, Rivers da kuma jihar Enugu.