Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bukaci kungiyoyin Yan aware dake Gabashin Jamhoriyar Dimokuradiyyar Congo da su aje makaman su tare da yin aiki da Gwamnati domin samun zaman lafiya Mai dorewa.
Wakilan kungiyoyin Yan aware akalla 20 ne suka halarci wata tattaunawa ta Kai tsaye da Jami’an gwamnatin DR Congo da ya gudana a Babban birnin kasar Kenya wato Nairobi
Tattaunawar dai na daya daga cikin kudurin da aka cimmawa a Taron sulhu da shugabannin kasashen Gabashin Afrika suka yi a baya-bayan nan.
Duk kungiyar da ta kauracewa Taron tattaunawar na sulhu, za ta fuskanci fushin matakin soji, kamar yadda aka sanar bayan Taron.
A karshen taron kuma kasashen Gabashin nahiyar Afrika sun amince da jibge jami’an sojin hadin guiwa a Gabashin kasar DR Congo domin magance Yan aware dake cigaba da kai farmaki a yankin.
A wani labari na daban.
PDP ta tantance Ƴan Takarar Sanatoci da Ƴan Majalisu a Lagos
Jam’iyyar PDP reshen Jahar Lagos a ranar Laraba ta tantance Ƴan Takarar Sanatoci, da Ƴan Majalisun Tarayya dana Jaha.
Tantance Ƴan Takarar Sanatoci Ƴan Majalisun Wakilai ya wakana a otel na Regency Dake GRA Ikeja a Lagos, a yayinda Ƴan Majalisu na Jaha ya wakana a otel na White House GRA a Ikeja, Lagos.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaru Hakeem Amode ya fitar mai kwanan watan 19 ga watan Afrilu na Shekarar 2022, ya nuna yadda Ƴan Takarar Sanatoci ake kira dasu biya Naira dubu 350,000 inda Ƴan Majalisun Tarayya ake karɓi Naira 200,000 daga hannun su.
Ƴan Majalisun Jaha ana karɓar Naira dubu 50,000, inda za’a karɓi Naira Dubu 500,000 daga Masu Takarar Gwamna, kuɗin Sashen Mulki.
Ƴan Takarar wanda suka iso wurin da misalin ƙarfe 9 na safe, an buƙace su dasu biya shaidar biyan kuɗin inda suka yi.
Duk da irin gargaɗin da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa Chief Olabode George Yayi akan irin waɗannan kuɗin.