Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sanar da dokar haramta mummunar aski da kuma sanya damammun kaya musamman Jeans.
Shugaban ya ce ya dauki wannan mataki ne don hana shigar da al’adar turawan yamma izuwa kasar, domin ya ga sun fara kokarin dauka.
Jaridar Rodong Sinmun ta kasar ta ruwaito cewa kasar na da dadadden tarihi dake nuni da cewa muddin yan kasar suka rungumi dabi’ar kasashen tamma to lallai ba da jimawa ba za ta wargaje duk da irin karfin mulki da tattalin arziki.
Ta kara da cewa dole ne idan ana bukatar dakatar da wannan ta’ada sai an hori matasa masu tasowa daga rungumar dabi’ar turawan yamma.
Sauran dokoki da ya kafa hwr da haramta rina gashin kai da kuma huda hanci, inda ya ce duk wanda ya kuskura aka kama shi da wannan mummuna dabi’a to zai dandana kudarsa.
A yanzu haka akwai nau’ukan aski guda goma sha biyar da dokar kasar ta tanada, inda duk wanda ya yi aski ba irinsu ba to babu makawa zai ɗanɗana Kuɗar shi, cewar Kim.