Mamallakin Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya baiwa jami’ar tarayya ta Dutsinma a jihar Katsina tallafin kyamarori guda biyu na Naira miliyan uku.
Haka-zalika, Farfesa Gwarzo ya ba jami’ar Dan Dicko Dan Koulodo dake Maradi da kuma ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jamhuriyar Nijar gudunmawar Kyamarorin guda daya kowacce.
Farfesa Gwarzo ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da yake mika kayayyakin ga Shugaban Jami’ar ta FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi a birnin Maradi na jamhuriyar Nijar a yau Laraba.
Shugaban MAAUN da kuma shugaban Jami’ar FUDMA na Maradi ne domin halartar bikin karrama sabbin daliban jami’ar Dan Dicko Dan Koulodo wanda ya gudana a Jiya Talata 22 ga watan Fabrairu.
Da yake karbar kayayyakin, shugaban Jami’ar ta FUDMA, Farfesa Armaya’u Bichi ya godewa Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin.