By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana alhininsa game da wani mummunan lamari da ya faru a Garin Alkali da ke karamar hukumar Bursari a jihar Yobe, inda aka ce an harbe wani direban mota har lahira.
Lamarin dai ya haifar da kazamar zanga-zanga a garin Gashua mai makwabtaka da hedikwatar karamar hukumar Bade ranar Asabar.
A cewar mai baiwa shugaban majalisar dattawa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, Lawan ya jajanta wa iyalan mamacin tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin da nufin gurfanar da duk wanda ke da hannu a kisan.
Awoniyi ya ruwaito Lawan yana cewa, “Na yi matukar bakin ciki da mummunan labarin da ya faru a Garin Alkali a ranar Asabar da kuma ta’addancin da suka biyo baya. Kisan direban da ba shi da laifi mugu ne kuma abin zargi ne. Bai kamata a yi la’akari da kowane dalili ba.
“Zuciyata tana tafe da dangin wanda abin ya shafa. Allah ya jikan su da rahama.
“Ina kira ga hukumomi da su binciki lamarin sosai da nufin gano dalilin da ya sa ya faru da kuma yadda ya faru da kuma sanya takunkumin da ya dace don dakile sake afkuwar lamarin nan gaba.
“Ina kuma kira da a kwantar da hankula tare da tabbatar wa al’umma masu son zaman lafiya cewa za a yi adalci a wannan lamarin.
“Ina kira ga al’umma da kada su taba daukar doka a hannunsu duk abin da zai tunzura su saboda irin wannan hali yakan haifar da ƙarin bala’i.”
Shugaban majalisar dattawan ya yabawa gwamnatin jihar Yobe da kuma ‘yan sanda bisa gaggauwa da suka yi wanda hakan ya taimaka wajen dakile matsalar cikin gaggawa tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’ummar da abin ya shafa.