Allah ya yi wa Farfesa Habu Galadima rasuwa. Har zuwa rasuwarsa, shi ne shugaban makarantar koyon dabaru da tsare-tsare na kasa, NIPSS dake Kuru a kusa da garin Jos.
Birgediya Janar C.F.J. Udaya, Sakatare kuma Daraktan gudanarwa na makarantar shi ne ya bayyana rasuwar shugaban makarantar a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a Jos.
A cewar Udaya, Galadima ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekara 57 a duniya.
Za a bizne shi bada jimawa ba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.