Alhaji Shuaibu Wakili, Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa na Jihar Katsina, ya bayyana cewa, duk da kukan da wasu ’yan Nijeriya ke yi a halin yanzu, watarana kuma za a yi kukan rashin sa bayan ya bar mulki, kamar yadda aka yi wa tsofaffin shugabannin kasar irinsu Marigayi Janar Sani Abacha.
Ya kuma ce, tunda ake mulki a Nijeriya, ba a taba samun Shugaban Kasar da ya kula da rayuwar talaka ba, kamar ta Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a irin kokarin tallafa wa kungiyoyin manoma a kasar, ya na mai cewa, idan da za a ce a iya gyaran kundin mulkin kasa, suna goyon bayan ya zarce a 2023, ya zama Shugaban Kasa na dindindin, “saboda duk ranar da ya bar mulki, wallahi talakawa sai sun yi kuka da idanunsu a kasar nan,” in ji shi.
Alhaji Wakili ya bayyana haka ne a lokacin ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishinsa dake kan titin Ibrahim Babangida a cikin birnin Katsina.
Shugaban Manoman Shinkafar ya cigaba da cewa, “duk wanda ya ce, akwai yunwa a kasar nan lokacin mulki Buhari, to ya dai fadi ra’ayinsa ne kawai, amma ba gaskiya ba ne. A lokacin da aka yi yunwa, duk yawan Katsina shago daya ko biyu ke da abinci. A yanzu haka ne? Amma na yadda a kasar nan akwai talauci, tattalin arziki na duniya ne ya kare, ba Nijeriya kadai ba ce.”
“A Kaka ana sayar da buhun masara Naira 16,000? Ba a taba ba, sai wannan gwamnati. Haka manomi na gona a bi ka da kudi da taki a ba ka. Idan manomi bai gode wa gwamnatin Buhari ba, ya saurari azabar Allah!”
Da ya juya kan matsalar tsaro, ya ce, “matsalar tsaro gadon ta muka yi a gwamnatin baya, kuma duk abinda Shugaban Kasa Buhari ya kamata ya yi, ya yi shi. Wani lokaci har da mutanen gari ake hadawa a yi wannan ta’addanci. Dole sai mun dage da addu’o’i ga gwamnati na ganin ta kawo karshensa.”
Daga karshe, Shugaban ya goyi baya bude kan iyakokin da Shugaba Buhari ya yi, yana mai cewa, “tun da har yanzu ba abinci za a dinga shigo da shi ba. Amma mun ji dadi da aka ce ban da abinci, ta karfafa mana gwiwar a fito a yi noma, kuma tuni al’umma suka amsa kiran. Mun shirya tsaf, domin yin wani shiri da za mu yi Dalar shinkafa.
“Shinkafar da muka noma ba ta da sinadari na daban, wadda ake shigowa da ita ana iya ajiye ta shekara biyar kuma sinadari ake sanya mata, shi ya sa ciwuka suka yi yawa a tsakanin al’umma. Mutane sama da dubu dari suka amfana da bashin noman shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta bai wa manoman shinkafa a jihar Katsina.
“Ba a taba gwamnati da take daukar kudi, ta ba wa manoman shinkafa da masara da rogo da kuma manoman kifi kamar wannan ba. Kusan kowa an ba shi duk a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Kukan da ’yan Nijeriya ke yi a yanzu, da ma sun saba yin sa, sun yi lokacin Babangida da Abacha, amma daga baya sun yabe su. Wallahi duk ranar da Buhari ya bar mulki, sai talakawan kasar nan sun yi kuka da idanunsu, musamman ma manoma.”
-Rahoton Leadership A Yau