By Abbas Yakubu Yaura
Babban Darakta Janar na masu yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya gargadi matasa masu yi wa kasa hidima dasu daina tafiye-tafiye cikin daddare domin gujewa hadurra ko kuma wani harin da akan iya kai musu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an yi garkuwa da wasu masu yiwa kasa hidima biyu a watan daya gabata a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a lokacin da suke tafiya sansanin horar da masu yi wa kasa hidima na NYSC.
Da yake magana a Abuja a wani taron manema labarai na sanar da ayyukan shirin kashi na (C) na shekarar 2021, yace shirin yana kuma aiki tare da hukumomin tsaro don tabbatar da cewa mambobin kungiyar sun kasance cikin koshin lafiya.Ibrahim ya kuma bayyana shirin da zai yi na tura kusan Naira miliyan 511 zuwa ga asusun tarayya na shekarar 2021.
Sannan yace a shekarar data gabata Hukumar NYSC ta aika da Naira miliyan 280 zuwa asusun tarayya inda yace kudaden da aka aika wata gudumawa ce ga tattalin arzikin kasa.
A ci gaba da gudanar da ayyukan sansanin Batch C kashi na 2, Ibrahim ya yi gargadin cewa kada wani wanda ya kammala karatun bogi ya zo a sansanonin wayar da kan jama’a domin za a tantance su kuma a hukunta su.