Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu zai bar kasar a ranar Laraba.
Ayu zai tafi zuwa Turai yayin da mataimakin shugaban jam’iyyar, Iliya Damagun, zai maye gurbinsa wajen jan ragamar Jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ban Yarda Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Ba — Okowa
Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa na Ayu, Simon Imobo-Tswam, ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, zai bar Najeriya zuwa Turai gobe Laraba.”
“Ayu zai shafe kusan makonni biyu a wajen kasa baya nan. Yayin da ya tafi, Mataimakin Shugaban (Arewa), Iliya Damagun, zai yi aiki a madadinsa.”
“Tuni shugaban Jam’iyyar na kasa ya mika takardar mulki ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.”
Kazalika ana sa ran zai dawo a karshen wannan watan da muke ciki.”
A wani labarin kuma, Tinubu Ba Marar Lafiya Bane, Yana Aiki Tsawon Sa’oi 20 A Kullum – Onanuga
Majalisar yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC a ranar Talata ta ce sabanin rade-radin da ake yi kan mai rike da tutar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, yana cikin koshin lafiya da hazaka.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sansanin tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana shugaban jam’iyyar APC na kasa a matsayin doki mai cin gashin kansa, wanda ke aiki tukuru na tsawon sa’o’i 20 a kullum.