• Shugaban rundunar yan sandan Nijeriya ya ziyarci gwamnan Abdullahi Umar Ganduje a fadar gwamnatin jihar.
• “Jihar Kano itace jiha mafi zaman lafiya a Najeriya” inji Usman Alkali
• “Nazo ganin kayayyakin tsaro ne na zamani da Ganduje ya Sanya a jihar Kano.” cewar IGP.
Mai girma gwamnan jihar Kano Dacta Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya karbi bakun cin, Shugaban rundunar yan sandan ta kasa Insfecta Janar Alkali Baba Usman, a wani ziyara da ya kai mai tare da wani babban jami’in dan sanda dake aiki a shelkwatar tsaro ta kasa, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Kano.
Shugaban rundunar ya zo Kano ne domin bikin yaye sabbin manyan Jami’an yan sanda masu mukamin ASP, karo na uku, a kwalejin horas da yan sandan dake Wudil.
Kazalika Usman Alkali, ya sami labarin irin, irin kokarin da gwamnatin jihar Kano ke yi a fannin tsaro, hakan ya sa ya tsawaita zaman shi a jihar da kwana daya, da nufin zagaya wa lungu da Sako na jihar, domin ganema idon shi, irin kayayyakin tsaro na zamani da gwamnan ya samar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Maganin Gargajiya ya kashe mutun 10 a jihar Kwara
A cewar sa, “Na kaiwa gwamnan ziyaran ne, domin yaba masa a kan kokarin da gwamnatin jihar keyi, wajan tabbatar da tsaro, da kasan cewar ta, jiha mafi yawan al’uma a kasar nan, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali” inji shi.
Lokacin da ya ke tarban bakin, Gwamna Ganduje, ya kasan ce, tare da Mataimakin shi Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, Shugaban yam’iyar APC na jihar Alhaji Abdullahi Abbas, Kwamishinan yada labarai na Kwamaret Muhammad Garba, da Kwamishinan kasafin kudi na jihar Nura Muhammad Dankadai, Shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan-Agundi, Babban mai bai wa gwamnan shawara a kan jami’an yan sandan al’uma Abm Muktar Gashah, Daractan aiyuka na Musamman Konel Malami, da kuma sauran jami’an gwamnatin jihar.