Da yake jawabin a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 a birnin New York, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi kira da a dage takunkumin da aka kakabawa Zimbabwe.
Shugaban kasar Senegal, kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu, ya ce matakan da ake dauka kan kasar Zimbabwe na kara ta’azzara al’ummar kasar cikin kangin talauci. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Amurka da Tarayyar Turai (EU) na ci gaba da kakaba wa Zimbabwe takunkumi, saboda rashin samun ci gaba a sauye-sauyen tsarin demokradiyya da hakkin dan Adam da kuma takaita yancin yan jarida da ake zargin shugabannin kasashen da yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Ariwoola A Matsayin Babban Alkalin Alkalai
Takunkuman dai sun ya shafi mutane da kamfanoni da suka hada da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa.
Rahotanni sun nuna cewa tattalin arzikin Zimbabwe ya fuskanci matsalolin a cikin yan shekarun da suka gabata tare da hauhawar farashin kayayyaki amma ana alakanta matsalolin ne da takunkuman da aka kakabawa kasar.
Haka kuma shugaba Macky Sall shi ne shugaban Afrika na farko da ya yi jawabi a zauren taron kawo hada wannan rahoton..
Shugaban kuma ya bukaci kwamitin sulhun da ya magance rikice-rikice a Afirka kamar yadda ya magance wasu rikice-rikice a fadin duniya.
Ya kuma yi kira da’a yiwa majalisar gyaran fuska wadda ta sa ta kasance mai cike da rudani da doba yuwuwar baiwa Afirka kujerar dindindin a zauren.
Mista Sall ya kuma yi kira da a bai wa Afirka kujera a cikin kungiyar G20 da ta kunshi shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a fadin duniya.
A halin da ake ciki kuma, ana sa ran karin wasu shugabannin kasashen Afirka za su yi jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba, rana ta biyu a zaman na muhawarar manyan jami’ai da shugabannin kasashen duniya.
A WANI LABARIN KUMA:Yajin Aikin ASUU: Sojoji Da ’Yan Sanda Sun Dakatar Da Zanga-zangar Dalibai
Jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda sun bazama a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja domin hana shugabannin kungiyoyin dalibai gudanar da zanga-zangar adawa da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Shugabannin kungiyar Dalibai daga cibiyoyi daban-daban na Kaduna sun yi barazanar tare babbar hanyar a yau a wani mataki na nuna fushinsu kan yajin aikin da ASUU ke yi a kasar.