Shugaban SMEDAN Dikko Raɗɗah ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Katsina
Tsohon Shugaban Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i na Ƙasa-SMEDAN Dr. Dikko Umar Raɗɗah ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna a Jam’iyyar APC a Jahar Katsina.
Shugaban Kula da Gudanar da Zaɓen daga uwar Jam’iyya ta Ƙasa Barista Kaka Shehu Lawan ya ayyana Dr. Dikko a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan ƙuri’u masu rinjaye daya samu fiye da sauran Ƴan Takara guda 9 da aka Fafata dasu a zaɓen.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ba Na Bukatar Karfi Kamar Ronaldo Wajen Jagoranci Najeriya – Tinubu
Ƴan Takara guda tara ne, aka fafata dasu a zaɓen fidda Gwani, wanda ya wakana a Filin wasa na Muhammdu Dikko dake Katsina.
Barista Kaka Shehu Lawan yace Dr. Umar Radda ya samu nasara a zaɓen, bayan ƙuri’u 506 da ya samu, wanda hakan ne ya tabbatar mashi da nasarar zaɓen.
Sai Tsohon Sakataren Gwamnatin Jahar Mustapha Inuwa ya samu ƙuri’u 442, sai Tsohon Shugaban Hukumar kula da Buga Kuɗi Abbas Umar Masanawa da kuri’a 436.
Sauran Ƴan Takarar da aka Fafata dasu sun ƙunshi Faruq Lawal Jobe mai ƙuri’a 71, da Ahmed Musa Dangiwa da kuri’a 220, a yayinda Mataimakin Gwamna ya samu Ƙuri’a 65.
Sai Sadiq Ƴar’adua Mai ƙuri’a 32, da Abdulkarim Dauda mai kuri’a 7.
Jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin Dan Takarar Gwamna, Dr. Umar Radda ya godema Allah a bisa wannan dama daya bashi na zama Ɗan Takarar Gwamna, sai ya alwashin ciyar da Jahar a matakin gaba, idan aka zaɓe shi.
Comments 1