Shugaban Tanzaniya John Magufuli ya fito a bainar jama’a yana kushe alluran rigakafin Korona da Turawan yamma suka sarrafa.
Duk da cewa kawo yanzu shugaban na Tanzaniya ya kasa kawo wata hujja da za ta gaskata ikirarin da yake yi, a ranar Laraba ya zargi mutanen kasar da suka yarda aka yi musu rigakafin Korona a ketare da cewa sune suka kawo wa Tanzaniya zango na biyu na Korona.
Magufuli ya ce idan da rigakafin Korona gaskiya ce da Turawa sun samar da rigakafin HIV/AIDS da Maleriya da kuma cutar daji, yana mai gargadin ‘yan Tanzaniya da kada su yarda Turawa su yi amfani da su wurin cimma wata manufa da sunan yaki da cutar Korona.
Tun daga tsakiyar shekarar da ta gabata dai lokacin da Tanzaniya ta sanar da cewa mutum 509 sun kamu da Korona, gwamnatin kasar ba ta sake sabunta adadin masu kamuwa da cutar ba.