Wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a jihar Zamfara, Bello Turji ya saki wasu mutane 52 da suka dade da yingarkuwa da su bisa radin kansu.
Turji shi ne shugaban masu kisa da garkuwa da mutane a Arewacin Zamfara da kuma kewayen kananan hukumomin Sabon Birni da Isah na jihar Sokoto.
Wannan Ci gaban bazai rasa nasaba da shirinsa na ajiye makamai da tsagaita wuta ta hanyar tattaunawa ba
An ce Bello Turji ya rubuta wasika zuwa ga Masarautar Shinkafi a watan Disambar da ya gabata yana mai jaddada aniyarsa ta ajiye makamai da kuma rungumar zaman lafiya.